BBC navigation

'Kwallon da Ibrahimovic ya ci babu irinta a tarihi'

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:03 GMT

Zlatan Ibrahimovic

Kocin Sweden, Erik Hamren, ya ce kwallo ta hudu da Zlatan Ibrahimovic ya zura lokacin wasan sada zumuntar da suka buga da Ingila ta yi masa kama da kallon majigi.

Erik Hamren ya ce, ''Kan da Zlatan ya sanya wa kwallon lokacin da ya zura ta hudu a wasan ya yi kamar ina kallon wasan bidiyo''.

Kyaftin din Ingila ma, Steven Gerrard, wanda ya buga wasansa na dari a Ingila, ya bayyana kwallon da Zlatan ya ci da cewa '' ita ce kwallo mafi kyawu da na taba ganin wani dan wasa ya zura a tarihi''.

Hamren ya ce: ''Bana tsammanin mutum zai kara ganin irin yadda aka zura kwallo kamar wannan a nan gaba''.

''Wani lokacin idan Zlatan yana cin kwallaye irin wadannan lokacin wasannin motsa jiki, sai ka ga kamar ba zai iya yin haka ba idan aka zo buga wasanni da kulob-kulob''.

Sweden ta ci hudu yayin da Ingila ta ci biyu a wasan sada zumuntar da suka yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.