BBC navigation

Kyaftin Abega na Kamaru ya riga mu gidan gaskiya

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:19 GMT
Tutar Indomitable Lions

Tutar Indomitable Lions na Kamaru

Tsohon Zakaran Kwallon Kafar Afirka Théophile Abega ya mutu yana da shekaru hamsin da takwas da haihuwa.

Dan wasan, wanda ya jagoranci tawagar 'yan kwallon kafar Kamaru da ta daga Kofin Kasashen Afirka a shekarar 1984 ya mutu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a Babban Asibitin Yaounde.

A shekarar ta 1984 da Abega ya jagoranci tawagar ta Kamaru ce kuma aka bayyana shi a matsayin Zakaran Kwallon Kafar Afirka.

Shekaru biyu kafin na kuwa ya taka leda a dukkan wasannin da tawagar Kamaru ta buga yayin fitar ta farko a Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya a 1982 a Spain.

Sai dai kuma salon wasansa a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka a 1984 a Abidjan ne, inda da ya ci kwallo a wasan karshen da Indomitable Lions suka lallasa Najeriya da ci uku da daya, ya kawo masa suna da daukaka.

Galibi Abega yayi wasa ne ga kungiyar kwallon kafa ta Canon Yaounde, wacce ya taimakwa ta lashe Gasar Zakarun Afirka a shekarun 1978 da 1980.

Daga bisani kuma ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Toulouse a Faransa da Vevey Sport ta Switzerland kafin ya yi ritaya yana da shekaru talatin da uku.

A rayuwarsa kuma, bayan kasancewa shugaban Canon Yaounde, ya rike mukamin magajin garin wata gunduma ta birnin Yaounde har tsawon shekaru hudu.

A watan jiya ya yi bayyanarsa ta karshe a bainar jama'a lokacin da ya ziyarci sansanin Indomitable Lions yayin da suke shirin buga wasansu da Cape Verde a yunkurinsu da bai yi nasara ba na samun gurbi a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka.

Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da dalilin mutuwarsa ba, wani dan uwansa ya bayyana cewa tun bayan wata tafiya ta kasuwanci da ya yi zuwa Amurka makwanni biyu da suka gabata yake kwance a asibiti.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.