BBC navigation

Hanawa Cisse buga wasa ya harzuka Newcastle

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:30 GMT

Papiss Cisse

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ta fusata matuka da matakin da hukumar kwallon kasar Senegal ta dauka na hana Papiss Cisse shiga wasan da ta yi da Swansea a Gasar Premier ranar Asabar.

Dan wasan gaban ya janye daga tawagar Senegal a wasan sada zumuntar da za ta buga da Nijar a makon da muke ciki, yana mai cewa yana fama da ciwon baya.

Senegal ta yi amfani da dokar hukumar Fifa ta hana dan wasa shiga wasa tsawon kwanaki biyar, bayan da ta yi ikirarin cewa ba a aike mata da cikakken bayani na halin da Cisse ke ciki ba.

Sai dai a wata sanarwar da ta fitar, Newcastle ta ce ta yi "mamaki da bakin ciki game da matakin da hukumar kwallon kafar Senegal ta dauka".

Kungiyar ta Newcastle ta ce tun lokacin da West Ham ta doke ta ranar Lahadin makon jiya ne ta shaidawa Senegal cewa Cisse ba zai samu damar bugawa kasarsa wasan da ta yi ranar Laraba ba, amma ba a ba su amsa ba.

A karkashin dokar Fifa wacce Senegal ta yi amfani da ita, tawagogin kwallon kafa na kasashe na da damar dakatar da dan wasa daga buga wasanni tsawon kwanaki biyar, idan ya ki buga musu wasa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.