BBC navigation

Zan daina kwallon Tennis idan ban samu kudi ba —Goodall

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:35 GMT

Josh Goodall

Dan kwallon tennis na biyu a Burtaniya, Josh Goodall, na duba yiwuwar yin ritaya daga wasan a badi saboda matsalar rashin kudi da yake fuskanta.

A cikin shekaru takwas da suka gabata, Goodall ya samu fam kusan dubu talatin ne kacal.

Goodall, wanda ke da shekaru 27 a duniya, yana matsayi na 232 a kwallon tennis na duniya; hakan yana nufin tsakaninsa da Andy Murray, dan kwallon tennis na daya a Burtaniyar, akwai mutane 229.

Goodall ya ce yana dada manyanta amma ba ya samun kudi da yawa, don haka ne ma ya ce idan a karshen kakar wasanni ta badi bai shiga jerin 'yan wasa 150 da ke sama ba, to lallai zai yi ritaya daga wasan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.