BBC navigation

Norwich sun cancanci nasarar da suka yi —Ferguson

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:25 GMT

Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya yabawa kwazon abokan hamayyarsa, Norwich, lokacin wasan da suka yi wanda suka ci United kwallo daya mai ban haushi.

A makon jiya dai Manchester United ce ke sama a kan teburin gasar, amma kwallon da dan wasan Norwich, Anthony Pilkington, ya zura ta dawo da United mataki na biyu a teburin gasar.

Ferguson ya ce, '' Sun cancanci nasarar da suka yi saboda sun yi kokari matuka. Sun kare gidansu sosai, kuma mai tsaron gidansu ya yi kokari sau biyu zuwa uku wajen hana 'yan wasanmu cin kwallo."

Sai dai duk da cewa United ta fado daga saman tebur da maki daya - a wasanni 11 cikin 18 da ta buga a kakar wasa ta bana - Ferguson ya ce yana da kwarin gwiwa kulob din zai tagaza nan gaba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.