BBC navigation

Martinez ya zargi Suarez da shurin dan wasa

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:44 GMT

Roberto Martinez

Kocin Wigan Roberto Martinez ya zargi dan wasan Liverpool Luis Suarez da take dan wasan kulob din lokacin da suke yin wasa.

Martinez ya yi ikirarin cewa Suarez ya shuri dan wasan gaba na Wigan, David Jones, ana mintuna 63 da fara wasan wanda Liverpool ta lallasa Wigan da ci 3 babu ko daya.

Martinez ya ce, "Suarez ya yi sa'a saboda alkalin wasa bai ga shurin da ya yi wa David Jones ba. Ban fada wa alkalin wasa ba. Ya kamata ya gani da kan sa. Idan da za a sake nuna wasan za ka ga shurin da Suarez ya yi wa dan wasan karara ''.

Suarez ne dai ya zura kwallaye biyu a ragar Wigan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Haka kuma shi ne ya taimakawa dan wasan da ya zura kwallo ta uku, lamarin da ya bai wa Liverpool damar yin nasara a wasan wanda aka buga a gidansu karo na biyu a kakar wasanni ta bana.

Kalaman da Martinez ya yi za su iya yin sanadiyar sanyawa Suarez idanu sosai duk lokacin da zai buga wasa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.