BBC navigation

Ba za mu sayar da Walcott yanzu ba - Wenger

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:40 GMT

Theo Walcott

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce ba zai sayar da dan wasan baya, Theo Walcott, a watan Janairu ba.

Hakan na nufin kulob din zai iya barin Walcott ya tafi a bazarar da ke tafe, bayan kwantiraginsa ta kare a karshen kakar wasanni ta bana.

Walcott na da damar sanya hannu a kwantiragi da wani kulob din a watan Janairu idan ba a sabunta kwantiraginsa a Arsenal ba.

Tattaunawa game da sabunta kwantiragin dan wasan ta cije, kuma da aka tambayi kocin Arsenal game da yiwuwar sayar da shi idan ba a cimma matsaya a shekarar 2013 ba, sai ya ce '' a'a''.

A watan Agusta Walcott ya ki sanya hannu a wani kwantiragin shekaru biyar wanda za a biya shi fam 75,000 a duk mako; ya bayyana cewa mai yiwuwa ya ci gaba da bugawa kulob din idan aka bar shi ya rika buga wasa a matsayin dan wasan gaba.

Ya zura kwallaye tara a wasanni 17 da ya fito, wadanda ya taka-rawa ta dan wasan baya.

Ya fi sauran 'yan wasan kulob din yawan zura kwallo.

Wenger, wanda ya ce dole ne Walcott ya ci gaba da yin hakuri a yunkurinsa na son komawa dan wasan gaba, ya bayyana kwarin gwiwar cewa dan wasan zai amince ya sabunta kwantiraginsa da kulob din.

Walcott ya koma Arsenal ne daga Southampton a shekarar 2006 a kan fam miliyan goma sha biyu da dubu dari biyar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.