BBC navigation

'Mario zai iya shiga sahun manyan 'yan wasa'

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 10:47 GMT

Mario Balotelli

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce dan wasan gaba na kungiyar Mario Balotelli zai iya zama daya daga cikin manyan 'yan wasan duniya idan ya kara kwazo wajen horo.

Balotelli na fuskantar gwaji don tabbatar da lafiyarsa gabanin wasan da kulob din zai fafata da Real Madrid ranar Laraba a Gasar cin kofin zakarun Turai.

Mancini ya ce : ''Yana da duk wadansu abubuwan da za su sa ya cancanci zama daya daga cikin manyan 'yan wasan duniya. Zai iya zama kamar Cristiano Ronaldo da Lionel Messi idan ya zage dantse''.

A watan Maris Mancini ya ce bai amince da Balotteli ba, wanda za a iya cewa mazari ne cikin 'yan wasan gaba.

''Zai iya zura kwallaye biyu a makon gobe, sannan a ba shi jan kati a wani makon'', in ji Mancini.

A cewarsa, Balotelli yana da saukin kai idan ba ya wasa, amma idan ya shiga filin wasa sai ya fara taurin kai.

Ya ce: ''Bai san muhimmancin da wasan kwallon kafa ke da shi a rayuwarsa ba. Ina fata zai gane muhimmancin hakan nan ba da dadewa ba''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.