BBC navigation

'Garabasar miliyoyi ga 'yan wasan Najeriya'

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 10:45 GMT

Shugaban NFF, Aminu Maigari

Hukumar Kwallon kafar Najeriya ta ce za ta bai wa kowanne dan wasan Super Eagles kimanin Naira miliyan goma sha uku idan tawagar ta lashe gasar cin kofin kasashen Afirka da za a yi a badi.

Kakakin hukumar, Ademola Olajire, ya ce za a bai wa kowanne dan wasa naira miliyan daya da dubu dari biyar da hamsin idan ya buga wasa a matakin rukuni, kana a kara masa miliyan biyu da dubu dari uku da ashirin da biyar idan suka kai wasan kusa da na kusa da na karshe, sannan a ba shi miliyan uku da dubu dari daya a wasan kusa da na karshe; yayin da za a ba shi naira miliyan uku da dubu dari takwas idan suka buga wasan karshe.

Sakataren hukumar, Musa Adamu, ya ce za a ba 'yan wasan wannan garabasa ce domin a karfafa musu gwiwa yadda za su sa Najeriya ta yi alfahari da su, sai dai ya ki bayyana hanyar da hukumar za ta bi don samo kudaden da za ta bai wa 'yan wasan.

Sau biyu Najeriya na lashe gasar cin kofin kasashen Afirka, sai dai ta gaza cancantar shiga gasar a shekarar 2012 duk da cewa tana da fitattun 'yan wasan da ke buga wasanni a kulob-kulob na kasashen Turai irinsu Ikechukwu Uche, da Joel Obi, da Peter Osaze Odemwingie,da Emmanuel Emenike, da Taye Taiwo da kuma Chinedu Obasi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.