BBC navigation

Takaitaccen tarihin Younes Belhanda

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:58 GMT
Younes Belhanda

Younes Belhanda yana tallafawa Montpellier na Faransa

Idan gwarzon duniya Zinedine Zidane ya yaba maka, babu shakka kana yin abin da ya dace - kuma babu shakka Younes Belhanda ba zai manta da kakar bana ba.

Dan wasan mai shekaru 22 na daya daga cikin muhimman 'yan wasan da suka taka rawar gani a nasarar da Montpellier ta samu, wurin lashe gasar Ligue 1 a karon farko cikin kusan shekaru 100 tun kafa kungiyar.

Da yake taka leda a matsayin takwaran Olivier Giroud, dan wasan na Morocco ya zira kwallaye 12 a wasanni 26 - bakwai daga ciki gab da za a kammala gasar bayan dawowarsa daga gasar cin kofin Afrika.

Ganin yadda yake da baiwa da kwarewa a fagen kwallo, Belhanda na daya daga cikin shahararrun 'yan wasan Morocco a gasar cin kofin Afrika ta 2012 - inda ya zira kwallo a wasansu da Nijar.

Sai dai rawar da ya taka a Montpellier ce ta haskaka shi inda ya shiga sahun 'yan wasa sha daya da suka fi kowa taka leda a gasar Ligue 1.

Ya kuma zamo dan wasa matashi da ya fi kowanne taka leda a gasar a bara.

Daga cikin wadanda suka taba lashe wannan kyautar a baya, sun hada da Eden Hazard da Franck Ribery da Thierry Henry da kuma Zidane da kansa, a don haka Belhanda na alfahari da ita.

Montpellier ba sa yin kokari sosai bana, amma tsohon dan wasan na tawagar matasa ta Faransa na ci gaba da haskakawa.

Ya zira kwallaye hudu a wasanni 10 a gasar League - da kuma kwallaye biyu a wasanni hudu na gasar cin kofin zakarun Turai, wacce yake halarta a karon farko.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.