BBC navigation

Benitez ya zama sabon kocin Chelsea

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:33 GMT

Rafael Benitez

Mahukunta a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea sun nada tsohon kocin Liverpool, Rafael Benitez, a matsayin sabon kocin-wucin-gadi na kulob din kafin karshen kakar wasa ta bana.

An sauke tsohon kocin kungiyar, Roberto Di Matteo, ne ranar Laraba bayan da kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta lallasa Chelsea da ci uku babu ko daya a wasan da suka buga a Gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Nadin da aka yi wa Benitez na wucin-gadi zai bai wa mai mallakin kungiyar, Roman Abramovich, damar yi wa tsohon kocin Barcelona, Pep Guardiola, tayin jan ragamar kungiyar a kakar wasa ta badi.

Benitez, mai shekaru 52 a duniya, shi ne mai horas da 'yan wasa na tara da kungiyar ta dauka aiki tun lokacin da ta koma hannun Abramovich a shekarar 2003.

Wata sanarwar da Chelsea ta fitar ta ce : ''Wanda ya mallaki kungiyar da kuma hukumar gudanarwarta sun yi ammana cewa Benitez mutum ne wanda ke da kwarewa sosai a babban mataki na kwallon kafa; wada zai iya tafiyar da kungiyar bisa muradinmu''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.