BBC navigation

Takaitaccen tarihin Demba Ba

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:55 GMT
Demba Ba

Demba Ba yana haskakawa sosai a Newcastle

Demba Ba ya nuna kwarin gwiwa da juriya da kwarewa wurin zira kwallaye abinda ya bashi damar kasance wa daya daga cikin 'yan wasan da ke haskakawa a Newcastle.

Kuma wannan ne yasa ya ja hankalin mutane da dama har ya kai ga samun gurbi a jerin 'yan wasan da za a kada kuri'a a kansu.

Dan wasan na kasar Senegal mai shekaru 27 ya taka rawar gani matuka tun lokacin da ya koma Newcastle daga West Ham a shekara ta 2011.

Ya zira kwallaye 16 a shekara ta farko inda ya kasance dan wasan da ya fi kowanne zira kwallaye a kulob din - abinda ya taimakawa Newcastle ta kare kakar a mataki na biyar, sannan ta samu damar shiga gasar cin kofin Europa.

Duk da cewa ba kowanne wasa aka fara da shi ba a kakar bana, Ba, ya zira kwallaye takwas a wasanni 12 da ya buga - inda ya zamo wanda ya fi kowa zira kwallaye a kulob din kuma na biyu a gasar baki daya.

Ba, wanda aka haifa a Faransa, ya fara takawa Senegal leda ne a wasanta da Tanzania a watan Yunin 2007, kuma ya zira kwallaye hudu a wasanni 16 da ya buga.

Yana cikin 'yan wasan gaba da kasar take da su, inda yake neman gindin zama tare da abokin wasansa na Newcastle Papiss Cisse da kuma Moussa Sow da Dame N'Doye da Moussa Konate.

Sai dai Ba da abokan wasansa ba za su halarci gasar cin kofin kasashen Afrika da za a yi a Afrika ta Kudu ba, bayan da aka ladaftar da kasar sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan wasan share fagen da suka buga da Ivory Coast.

A maimakon haka, Demba Ba zai yi kokarin ganin cewa ya taimakawa Newcastle ta dago sama a teburin gasar Premier ta bana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.