BBC navigation

Drogba na so FIFA ta ba shi izinin tafiya aro

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:28 GMT
Drogba yana so fifa ta ba da aron sa

Didier Drogba

Tsohon dan wasan gaba na Chelsea, Didier Drogba, yana so FIFA ta amince masa ya samu kungiyar da za ta karbi aron sa daga kungiyar kasar Sin, Shanghai Shenhua.

Drogba yana neman amincewar FIFA a kan batun ne kasancewa bukatar tasa ta zo ne bayan an rufe kasuwar 'yan wasa.

Ana ganin Drogba yana so ne ya bugawa wata sabuwar kungiya wasa, yadda zai samu damar shiryawa gabanin Gasar cin kofin kasashen Afirka da za a yi a shekarar 2013, ganin cewa an kammala kakar wasanni a kungiyar Shanghai Shenhua.

Wata sawnarwa daga FIFA ta ce jami'anta na duba yiwuwar amincewa da bukatar da Drogba ya mika mata.

Har yanzu dai ba a san kungiyar da Drogba ke son komawa ba, sai dai a baya an yi ta rade-radin cewa zai koma Marseille, kungiyar da ya bari gabanin komawarsa Chelsea a shekarar 2004.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.