BBC navigation

Takaitacen tarihin Yaya Toure

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:02 GMT
Yaya Toure

Yaya Toure yana kan ganiyarsa a Man City da Ivory Coast

Bayan da ya tallafawa Manchester City ta lashe kofi a karon farko cikin shekaru 35, inda ya zira kwallo daya tilo a wasan da suka lashe kofin FA a Wembley.

Yaya Toure, ya kuma taka rawar gani wurin taimakawa Man City lashe gasar Premier a karon farko.

Dan wasan tsakiyar na Ivory Coast na sahun gaba wurin kawo karshen shekaru 44 da City ta shafe ba tare da lashe gasar League ba.

Toure ya taka rawar gani a wasan da Man City ta doke abokan hamayyarta Manchester United, sannan ya zira kwallaye biyu a wasan da suka doke Newcastle da 2-0.

Wannan ne kofi na baya-bayan nan da dan wasan mai shekaru 29 ya dauka, bayan da ya lashe gasar zakarun Turai,
Super Cup, kofin kulob din zakarun duniya, gasar La Liga ta Spain da Copa del Rey da ya lashe a Barcelona da kuma gasar League ta Girka da ya lashe da Olympiakos.

Toure, wanda ya lashe kyautar zakaran dan kwallon Afrika na Hukumar kula da kwallon kafa ta Caf a 2011, ya fara kakar bana da kafar dama.

Ya zira kwallo a wasan da City ta doke Chelsea a gasar cin kofin Community Shield, sannan ya zira karin kwallaye hudu a gasar Premier.

A watan Janairu, zai yi kokarin ganin ya lashe gasar cin kofin Afrika da tawagar Ivory Coast.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.