BBC navigation

"Za mu ci gaba da yiwa Benitez ihu"

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:52 GMT
Rafael Benitez

Rafael Benitez

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea sun ce za su ci gaba da yiwa kocin riko Rafael Benitez ihu har karshen kakar wasanni ta bana.

Ranar Lahadi aka yiwa Benitez ihu da ele yayin wasan da Chelsea ta buga da Manchetser City wanda aka tashi canjaras, ba ci.

Shugabar Kungiyar Magoya Bayan Chelsea, Trizia Fiorellino, ta ce, "Muna so masu wuka-da-nama a kungiyar su san cewa ba ma son shi".

Tsohon kocin na Liverpool ya karbi jagorancin Chelsea ne daga Roberto Di Matteo, wanda aka kora bayan kungiyar ta sha kashi a hannun Juventus a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Bayan canjaras din da kungiyar ta yi ranar Lahadi, Benitez ya ce zai sauya tunanin magoya bayan kungiyar a kansa ta hanyar cin wasanni.

Amma Fiorellino cewa ta yi: "Benitez ba shi da farin jini kuma ba zai yi farin jini ba iya tsawon zamaninsa".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.