BBC navigation

Brazil 2014: Aikin filayen wasa

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:43 GMT
Jerome Valcke

Babban Sakataren hukumar FIFA, Jerome Valcke

Babban Sakataren Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ya ce za a kammala aikin dukkanin filayen wasa goma sha biyu a fadin Brazil kafin lokacin da za a fara Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ta 2014.

Sai dai kuma Jerome Valcke ya shaidawa mahalarta wani taro a birnin Rio na kasar ta Brazil cewa ana samun tsaiko a sauran ayyukan shirin gasar.

Mista Valcke, wanda ke lura da ci gaban da ake samu a shirye-shiryen gasar ta Brazil, ya koka da karancin otal-otal din za a saukar da 'yan kallo daga kasashen waje wadanda aka kiyasta za su kai dubu dari biyar.

Ya kuma ce yanzu dangantaka ta inganta tsakanin hukumar FIFA da hukumomin kwallon kafa na Brazil.

A da dai Mista Valcke ya fusata jami'an kasar ta Brazil saboda ya nuna cewa ba za a iya kammala aikin filayen wasan ba.

Brazil za ta kashe dala biliyan goma sha biyar wajen samar da abubuwan da ake bukata don karbar bakuncin Gasar ta cin Kofin Duniya, wadanda suka hada da sababbin filayen wasa ko wadanda aka yiwa kwaskwarima guda goma sha biyu, da sababbin hanyoyin motocin safa, da kuma fadadaddun filayen saukar jiragen sama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.