BBC navigation

Najeriya ba za ta dauki Sidney ba

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:14 GMT
Sidney Sam

Sidney Sam ya ce a shirye yake ya bugawa Najeriya

Najeriya ta ce ba za ta samu dama ba ta saka tsohon dan wasan tawagar matasan Jamus Sidney Sam a cikin 'yan wasan da za su bugawa Super Eagles a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka badi.

Mahaifiyar dan wasan mai shekaru ashirin da hudu, wanda kuma ke bugawa kungiyar Bayer Leverkusen ta Jamus wasa, Bajamushiya ce, amma mahaifinsa dan Lagos ne.

Kasancewar bai taba bugawa Jamus cikakken wasa a matakin kasa-da-kasa ba, Sam na da damar bugawa Najeriya, amma fa idan Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta amince da sauyin kasarsa ta asali.

Makwanni biyu da suka wuce Sam ya ce a shirye yake ya bugawa Najeriya, bayan wata tattaunawa da suka yi da kocin Super Eagles, Stephen Keshi.

Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, ta ce ba ta da isasshen lokacin yiwa dan wasan rajista kafin fara Gasar ta Cin Kofin Afirka a Afirka ta Kudu ranar 19 ga watan Janairu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.