BBC navigation

Zan ba Najeriya rai na —Moses

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:33 GMT
Victor Moses

Victor Moses ya ce zai sadaukar da ransa ga Najeriya

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Victor Moses ya ce tuni hankalinsa ya koma kan rawar da zai taka a tawagar kwallon kafa ta Najeriya wacce za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka.

Yayin gasar da za a yi a Afirka ta Kudu dai, dan wasan ba zai buga wa kungiyar Chelsea wasanni ba har tsawon makwanni shida, amma ya nuna farin cikinsa matuka da samun damar bugawa kasarsa wasa a gasar a karo na farko.

Shafin intanet na wasanni Goal.com ya ambato dan wasan yana cewa: "Ba shakka wannan ne karo na farko da zan buga wasa a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka; kuma ina so wannan gasa ta zama wadda ba zan taba mantawa da ita ba ta hanyar sadaukar da duk abin da nake da shi ga Najeriya".

Ya kuma kara da cewa yana alfahari da samun damar wakiltar Najeriya a wannan mataki na harkar kwallon kafar Afirka.

"Zan yi amfani da kwarewar [da na samu] a kungiyoyin kwallon kafa [na Turai] don taka wa Najeriya leda a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2013", inji Moses.

"Ina so in sadaukar da komai a dukkan wasannin da zan buga, kuma na san sauran 'yan wasan da za a zaba ma a shirye suke su sadaukar da rayukansu ga Najeriya idan bukatar hakan ta taso".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.