BBC navigation

Beckham zai gana da Monaco

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:34 GMT
David Beckham

David Beckham

Tsohon kyaftin tawagar kwallon kafa ta Ingila, David Beckham, na shirin fara tattaunawa da kungiyar AS Monaco ta Faransa; ana kuma sa ran za a yi wata ganawa ranar Asabar bayan wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Amurka, MLS.

An bayar da rahoton cewa dan wasan mai shekaru talatin da bakwai a duniya na duba yiwuwar komawa kungiyar ta Monaco, tun bayan da ya sanar da cewa zai bar Los Angeles Galaxy.

Kungiyoyin kwallon kafa daga Rasha da Brazil ma sun nuna sha'awarsu ta sayen dan wasan.

Sai a farkon sabuwar shekara dai Beckham zai yanke shawara ta karshe.

Monaco dai na wasa ne a gasa mai daraja ta biyu a Faransa, wato Ligue 2, bayan ta rikito daga gasa mai daraja ta daya, wato Ligue 1, a shekarar 2011.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.