South Africa 2013: Kwanaki 50 kafin fara gasar

South Africa 2013: Kwanaki 50 kafin fara gasar
Image caption Kasashe 16 ne za su taka leda a gasar ta 2013.

Nan da kwanaki hamsin, ranar Asabar 19 ga watan Janairu 2013, 'yan wasan Afrika ta Kudu za su fara kokarin lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afrika a karo na biyu.

Bafana Bafana za su kara da sabbin fuska a gasar Cape Verde a filin wasa na Soccer City a Soweto, kafin daga bisani su fafata da Angola da kuma Morocco a rukunin.

Sauran kasashen 15 za su taka leda a gasar karo na 29 wacce aka fara a shekara ta 1957 da kasashe uku.

Afrika ta Kudu ta samu yabo kan yadda ta shirya gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010, kasar farko a Afrika da ta yi hakan, da kuma yadda ta gina sabbin filayen wasanni.

"Tara cikin goma" makin da shugaban Fifa Sepp Blatter ya basu.... "Mun cimma manufofinmu", kamar yadda shugaba Jacob Zuma ya bugi kirji...."masu kokonto ma yanzu sun amince" a cewar Danny Jordaan, wanda ya jagoranci shirya gasar.

Asusun Fifa ya fara aiki

A yanzu da ake shirin gudanar da wata gasar, ko wasan kwallon kafa ya samu ci gaba watanni 28 tun bayan da kyaftin din Spain Iker Casillas ya daga kofin duniya a birnin Johannesburg.

"...Afrika ta Kudu na da matasan 'yan wasa, kociyoyin ne ke bukatar horaswa... ajininsu yake su taka leda kamar Barcelona," a cewar Cavin Johnson, kocin Platinum Stars.

Sai dai a shekaru shida da suka gabata, kuloblukan Afrika ta Kudu basu kai ga zagayen kwata final ba a gasar zakarun Afrika.

Kuma tawagar kasar ta yi kasa da mataki 18 a jerin kasashen da suka fi hazaka na FIFA tun bayan gasar ta duniya.

Akwai dai asusun Fifa na bunkasa wasa da ilimi da fannin lafiya, wanda shi ne irinsa na farko...Fifa ta ce za ta samar da sabbin filayen wasanni 52.

Gasar Premier ta Afrika ta Kudu, na samun dala miliyan 277 daga kudaden talabijin, duk da cewa gasar Premier ta Ingila na da tasiri a kasar.

Ganin cewa akwai dokar da ta kayyade adadin 'yan kasashen waje zuwa biyar ga kowanne kulob a gasar.

Shin ko Afrika ta Kudu na samar da kwararrun matasan 'yan wasa?

"Gasar Premier ta Afrika ta Kudu babbar gasa ce, amma akwai karancin horas da matasa, ana bukatar shawo kan matsaloli, kamar horas da kociyoyi", a cewar Roger Palmgren, tsohon kocin AmaZulu FC.

Sauran kalubale

Kafin Afrika ta Kudu ta kai ga lashe gasar a karo na biyu, sai ta kawar da manyan kasashen da suka mamaye fagen kwallon Afrika.

Ivory Coast ce kan gaba, inda Didier Drogba ke kokarin lashe gasar bayan da suka sha kashi a bugun fanareti a wasan karshe na gasar da ta gabata a hannun Zambia.

Najeriya da Ghana sun dade basu lashe gasar ba - rabon Ghana da ta dauki gasar tun shekarar 1982, ita kuwa Najeriya tun shekara ta 1994.

Karin bayani