Takaddama tsakanin Ethiopia da Eritrea

Takaddama tsakanin Ethiopia da Eritrea

Kasar Ethiopia ta nemi hukumar kwallon Afrika ta CAF da ta sauya wurin da za a buga wasan share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afrika da za ta yi da Eritrea.

Ethiopia na son a dauke wasan daga Eritrea zuwa wata kasar ta daban.

Bukatar ta zo ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke ci gaba da takaddama kan batun iyakoki.

An tsara kasashen biyu za su fafata a Asmara, babban birnin Eritrea, tsakanin 14-16 ga watan Janairu, inda za a yi zagaye na biyu a birnin Addis Ababa makonni biyu bayan haka.

Sai dai Ethiopia ta ce ba za ta je kasar Eritrea ba.

"Muna son a buga wannan wasa, sai dai bama so mu je Eritrea, kuma a bayyane take cewa gwamnatinsu ba za ta barsu su zo Ethiopia ba," a cewar mai magana da yawun hukumar kwallon Ethiopia Melaku Ayele.

"Adon haka muna bayar da shawarar a buga dukkan wasannin biyu a kasar Sudan da ke makwaftaka da mu."