Man U za ta kara da West Ham a gasar FA

Kofin gasar wasannin kwallon kafa na Nahiyar Turai

Manchester United za ta kece raini da West Ham United a filin wasa na Upton Park a zagaye na uku na gasar cin kofin FA.

Wannan daya ce daga cikin karawa hudu da kungiyoyin gasar Premier za su yi a tsakaninsu.

Southampton za ta karbi bakuncin masu rike da kanbun Chelsea, sai QPR da za ta fafata da West Brom, yayin da Arsenal za ta garzaya Swansea.

Manchester City za ta kara da Watford, yayin da Tottenham za ta hadu da Coventry a maimaicin wasan karshe na shekara ta 1987.

Kulob din Harrogate ko Hastings wadanda basu kai matsayin taka leda a gasar League ba za su kara da Middlesbrough, yayin da Lincoln ko Mansfield za su karbi bakuncin Liverpool.

Za a buga wasannin ne a ranakun Asabar 5 da kuma Lahadi 6 ga watan Janairun 2013.

Wasu daga cikin wasannin na FA

Crystal Palace v Stoke City

Brighton and Hove Albion v Newcastle United

Wigan Athletic v Bournemouth

Fulham v Blackpool

Aston Villa v Ipswich Town

Charlton Athletic v Huddersfield Town

Barrow or Macclesfield Town v Cardiff City

Barnsley v Burnley

Leicester City v Burton Albion

Millwall v Preston North End

Cheltenham Town or Hereford United v Everton

Derby County v Tranmere Rovers

Crawley Town v Reading

Aldershot Town v Rotherham United or Notts County

Accrington Stanley or Oxford United v Sheffield United