Martinez ya yi korafi kan jan kati

Kocin Wigan Roberto Martinez
Image caption Wigan ta sha kashi a hannun Newcastle da ci 3-0

Kocin Wigan Roberto Martinez zai duba yiwuwar daukaka kara kan jan katin da aka baiwa Maynor Figueroa a wasan da suka sha kashi a hannun Newcastle da ci 3-0.

An baiwa dan wasan na baya jan kati bayan da ya tade Papiss Cisse abinda ya kai ga kwallon farko ta bugun fanareti.

Da aka tambaye shi ko zai daukaka kara, sai Martinez yace: "Za mu duba.

"Fanareti da kuma jan kati ya yi yawa. Ina ganin matakin ya yi tsauri."

Ya kara da cewa: "Wannan babban lamari ne, ba za ka yanke hukunci ba tukunna sai kana da tabbaci."

Figueroa ba zai buga wasan da Wigan za ta yi ranar Asabar da Queens Park Rangers ba.

Haka shi ma dan wasan baya Gary Caldwell, bayan da ya samu katin gargadi sau biyar a kakar bana.

Honduran Figueroa shi ne dan wasa na karshe a bayan Wigan lokacin da Cisse ya yi kokarin wucewa da kwallon.

A sakamakon fanaretin da aka samu ne Demba Ba ya zira wa Newcastle kwallonsu ta farko.

Karin bayani