Mwelo ya soki Adebayor da Pienaar

Emmanuel Adebayor
Image caption Adebayor na barazanar kauracewa Togo saboda rashin jituwa da hukumar kwallon kasar

Shugaban kwamitin shirya gasar cin kofin kasashen Afrika ya soki Steven Pienaar, Emmanuel Adebayor da Samba Diakite da nuna son zuciya da "girman kai".

Dan wasan Everton Pienaar ya ce ba zai dawo daga ritayar da yayi ta bugawa Afrika ta Kudu kwallo ba domin taka leda a gasar ta 2013.

Shi kuwa Adebayor yana barazanar kauracewa tawagar Togo ne sakamakon rashin jituwar da ke tsakaninsa da hukumar kwallon kasar.

Yayin da Samba Diakite ya ce ya gwammace ya ci gaba da zama a QPR domin ya tallafa musu fita daga cikin halin tsaka-mai-wuyar da suke ciki.

Chief Mwelo ya shaida wa BBC cewa: "Bai kamata ace wani dan wasa da aka horas a Afrika ya ce yafi son kulob dinsa ba, a gani na wannan son zuciya ne da kuma girman kai.

"Kuma wadannan 'yan wasan da suke kaurace mana, ba su da wata makoma mai kyau saboda suna watsi da tsatsonsu."

Karin bayani