'Yan wasan Eritrea sun yi batan dabo a Uganda

tutar_kasar_eritrea
Image caption tutar_kasar_eritrea

Hukumar kwallon kafa ta Uganda da jami'an tsaron kasar sun kaddamar da wani bincike, domin gano inda wasu 'yan wasan Eritrea suka shiga, wadanda aka yi ammana cewa sun tsere ne.

Bayan an fitar da 'yan wasan daga gasar cin kofin Cecafa a Kamfala, 'yan wasan 17 da kuma likita mai duba lafiyarsu sun yi batan dabo.

Biyar da 'yan wasan da kuma jami'ai biyu ne kadai suka shiga mota kirar Bas data dauke su daga otal dinsu zuwa filin jirgin sama domin shiga jirgi zuwa Asmara a ranar Talata.

'' Bamu san inda 'yan uwan mu suke ba,'' inji kocin 'yan wasan Teklit Negash.

Mataimakin shugaban Fufa mai kula da matasa, Ptrik Ogwel ya tabbatar da batan mambobin kungiyar kwallon kafar ta Eriteria, ya kuma sha alwashi cewa 'Za mu nemo so duk inda suka buya. ''

Babban jami'in Fufa Edgar Watson ya ce za a sanya hotunan su a cikin jaridu saboda a yi saurin gane inda suke.

''Za mu nemo su, saboda ba su yi nisa ba.''

An fidda 'Yan wasan Eriteria daga gasar ne bayan da suka yi kunnen doki da Zanzibir da ci ba ko daya, kuma a wasan su da Malawi an tashi da ci 3-2, haka kuma sun sha kaye a wasan su na karshe da Rwanda, inda aka tashi da 2 da nema a ranar Lahadi.

Manajan Hotel din Sky Sylvia Nakamya inda 'yan wasan suke zauna ta bayyana cewa 'yan wasan sun fita a ranar lahadi da nufin za su je sayayya, amma sha biyu daga cikin su ne kadai suka dawo.

Sylvia ta kara da cewa'' daga baya biyar daga cikin wadanda suka dawo sun fito a cewarsu za su ziyarci abokansu, kuma basu dawo ba.''

Hakan ta taba faruwa a shekarar 2010 bayan kammala wasan Cecafa a Tanzania, 'yan wasa goma sha uku daga cikin 'yan wasan Eriteria sun bace tare da sauya sheka.

Da yawa daga cikin wadannan 'yan wasa sun kare a birnin Houston da kuma Texas akarkashin shirin Amurka na 'yan gudun hijira.