Libya na neman in horar da 'yan wasanta-Giresse

Image caption Allain Giresse, tsohon kocin Gabon da Mali

Tsohon Kocin kasashen Gabon da Mali ya ce Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar Libya ta yi masa horarda 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar.

Amma Bafaranshen Allain Giresse ya ce har yanzu ba su cimma wata yarjejeniya ba kan batun.

Wasu rahotanni daga Libya dai na cewa Giresse zai je kasar a makon gobe, domin kammala tattaunawar.

Tsohon dan wasan na kasar Faransa ya jagoranci Mali zuwa ga lashe matsayi na uku a Gasar Cin kofin Nahiyar Afrika da aka yi a farkon wannan shekarar, a kasashen Equatorial Guinea da Gabon.

Ya yanke shawarar kin sabunta kwantaraginsa ne da Mali a watan Mayu, bayan sun kasa daidaitawa kan wasu sabbin bukatu, daga hukumar kwallon kafa ta kasar.

Karin bayani