An dakatar da Mikel wasanni uku

Image caption John Mikel Obi yana yiwa alkalin wasa Clattenburg magana

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta sakawa dan wasan Chelsea John Mike Obi haramcin buga wasanni uku da kuma tarar Fam dubu sittin saboda yiwa alkalin wasa Mark Clattenburg barazana.

Mikel dan asalin Najeriya ya amsa aikata laifin a cikin wani lamari da ya faru a dakin sauya kaya na alkalin wasan, a karshen wasan da Chelsea ta buga da Manchester United ranar 28 ga watan Oktoba.

A wajen wani zaman bahasi da yayi ranar alhamis, kwamitin kula da'a mai zaman kansa na Hukumar ya amsa cewar Mikel yayi amanna cewar alkalin wasan ne ya yi kalaman nuna masa wariyar launin fata.

Sai dai kuma hukumar ta binciki zargin inda tace ta gano alkalin wasan baya da wasu tambayoyin da zai amsa.