Na gamsu duk da an doke mu - Sir Alex

Image caption Sir Alex Ferguson, kocin Man. United

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce ya gamsu da yadda matasan 'yan wasansa suka buga wasa a karawar da kungiyar ta yi da CFR Cluj, duk da doke ta da aka yi a wasan ta gasar Zakarrun Turai.

Kulod din na Man'U wanda dama ya riga ya wuce zuwa matakin kwata Fiyinal na gasar, ya zuba 'yan wasa masu rauni ne inda Wayne Rooney ne kawai aka saka daga cikin 'yan wasan da suka doke Reading a wasansu ta gasar Premier.

Ferguson yace kungiyar ta samu abin da ta so ta samu duk da cewar bata samu nasara ba, wato baiwa sabbin 'yan wasa damar gogewa da kuma gwada wadanda suka dawo daga jinyar raunukka.

Wannan dai shi ne karon farko da United ta kasa samun nasara a filin wasanta na Old Trafford tun bayan da 'yan wasan Rangers suka rike ta kunnen doki a shekara ta 2010.

Karin bayani