'Na ji dadi da Adebayor ba zai buga wa Togo wasa ba'

Image caption Dan wasan Tottenham Emmanuel Adebayor

Manajan kulob din Tottenham Hotspur Andre Villa-Boas ya ce yana farin ciki da kasancewar Emmanuel Adebayo ba zai buga wa Togo wasa ba a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika a watan Janairu.

Villa-Boas yace kungiyar sa za ta amfana sosai daga wannan shawarar da Adebayor ya yanke.

Jami'in Hulda da jama'a na dan wasan Ademoji Blaise ya fada ranar litinin cewar dan wasan ya dakatarda bugawa kasar sa wasa.

Adebayor wanda shi ne Kyaftin din kasar ta Togo ya shiga takon-saka da hukumar kwallon kafa ta kasar tasa ne kan kudaden ake biyan dan wasa bayan buga wasa.

Togo za ta shiga gasar ne a karon farko tun bayan da ta janye daga gasar ta shekarar 2010 a Angola bayan kai wani harin ta'addanci kan motar 'yan wasanta.

Adebayor ya yi murabus daga bugawa wasar kasa da kasa bayan wancan harin, amma ya amince ya taimakawa kasar ta samu cancantar shiga wannan gasar da za a yi a kasar Afrika ta Kudu.