Terry ba zai buga gasar zakarun duniya ba

John Terry
Image caption John Terry ya samu rauni ne a wasansu da Liverpool

Kyaftin din Chelsea John Terry ba zai buga gasar cin kofin zakarun duniya da za a yi a Japan ba saboda matsalar raunin da yake fama da shi a gwiwarsa.

Zakarun na Turai za su shafe kwanaki 11 ba tare da taka leda a gasar Premier ba suna wakiltar Turai a mako mai zuwa.

Da farko an yi zaton Terry zai shafe makonni uku ne bayan raunin da ya samu a watan Nuwamba.

Sai dai kocin Chelsea Rafael Bentiez ya ce: "Yaso yaje ya taimaka, amma zai fi kyau idan ya zauna. Zaman jirgi ba zai taimakawa rauninsa ba, a don haka gwanda ya zauna a gida."

Terry, mai shekaru 31, ya samu rauni a gwiwarsa ne a wasan da Chelsea ta tashi 1-1 da Liverpool.

Chelsea za ta kara da Sunderland ranar Asabar kafin su tafi Japan domin karawa da zakarun sassan duniya na Fifa guda shida.

Za su shiga gasar ne a wasan kusa da na karshe inda za su hadu da Monterrey na Mexico ko Ulsan Hyundai na Koriya ta Kudu a ranar 13 ga watan Disamba.