Messi ya sake kafa tarihi a duniya

Messi ya sake kafa tarihi a duniya
Image caption Messi ya cimma bajintar ne bayan da ya zira kwallaye biyu a wasansu da Real Betis

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya sake kafa tarihi a fagen tamolar duniya, inda ya zira kwallaye 86 a shekara ta 2012.

Dan wasan mai shekaru 25 ya haura adadin kwallaye 85 da Gerd Mueller ya zira a shekara ta 1972 - domin kafa sabon tarihi wanda ya hada da kwallayen da aka zira a kulob da kuma kasa.

Messi ya yi wannan bajinta ne bayan da ya zira kwallaye biyu a wasan da suka lashe Real Betis da ci 2-1 ranar Lahadi.

Ya zira kwallo ta farko ne a minti na 16 inda ya kamo Mueller, sannan ya zira ta biyu a minti na 25 abinda ya bashi damar kafa tarihi.

Akan hanyarsa ta cimma wannan bajinta, Messi ya zira kwallaye 74 a Barcelona da kuma 12 a Argentina a wasanni 66.

Har yanzu yana da sauran wasanni biyu a League da kuma daya a King's Cup kafin shekarar ta kare.

Mueller ya zira kwallaye 72 a Bayern Munich da 13 a West Germany lokacin da ya kafa nasa tarihin a shekarar 1972, kuma yana dan shekaru 27 a lokacin.

Karin bayani