Jacques Anouma zai kalubalanci Caf

Image caption Jacques Anouma

Daya daga cikin jami'an da ke wakiltar Afrika a Fifa Jacques Anouma, ya soki dokar Hukumar kwallon Afrika wato Caf da ta hana mishi tsayawa takarar shugabancin hukumar.

Ya bayyana dokar da Caf a matsayin 'abun kunya' wanda ya kawowa kwallon kafa koma baya a nahiyar Afrika.

Caf dai ta yanke shawarar cewa Issa Hayatou ne wanda ya jagoranci kungiyar tun daga shekarar 1987 zai tsaya takarar shugabancin hukumar a zaben da zata gudanar a watan Mayun badi.

Hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast ce ta bada sunan Anouma a matsayin wanda zai yi takara daga kasar, amma dokar Caf ta haramta masa yin takara saboda baya cikin membobin kwamitin gudanarwa na hukumar.

A wata sanarwa daya fitar a shafinsa na Internet, Anouma ya soki Caf, inda yace zai kalubalanci tsarin hukumar.

Anouma dai ya zargi Issa Hayatou da shirya manakisar hanashi tsaya takara domin ya ci gaba da mulkin kama karya a hukumar.