'Babu mai hamayya da Isa Hayatou'

Isa Hayatou
Image caption Hayatou ya shafe shekara da shekaru yana shugabancin Caf

A yanzu ta tabbata cewa babu wanda zai kalubalanci shugaban hukumar kwallon Afrika Isa Hayatou a zaben shugabancin hukumar da za a yi.

A wani taro da aka gudanar a ranar 10 ga watan Disamba, Caf ta shaida wa kwamitin gudanarwar hukumar cewa Mr Hayatou shi kadai ne dan takara a zaben.

Dan kwamitin zartarwa na Fifa Jacques Anouma, ya ce zai mika sunansa domin kalubalantar Mr Hayatou.

Za a gudanar da zaben ne a watan Maris mai zuwa a birnin Marrakech, na kasar Morocco.

Wannan kuwa na faruwa ne duk da cewa an haramta wa dan kasar ta Ivory Coast damar shiga takarar a watan Satumbar da ya gabata.

Sakamakon sauye-sauyen da Hataou, dan shekaru 66, ya jagoranta da suka ce mambobin kwamitin zartarwar Caf din ne kawai ke da izinin tsayawa takarar shugabancin.

Duk da cewa an mika sunan dan shekaru 60 din domin tsayawa takara kafin ranar 9 ga watan Disamba kamar yadda ka'idojin zabe suka nuna, amma bai fito a jerin sunayen 'yan takarar da Caf ta wallafa a shafinta na intanet ba.

Karin bayani