Tsarin tsayuwa a filin wasa a Ingila

Tsarin tsayuwa a filin wasa a Ingila
Image caption A baya dai an soke tsarin saboda tashin hankalin da ya faru na Hillsborugh

Wata gammayar kungiyar magoya bayan kwallon kafa ta ce Kungiyoyi goma sha daya a Ingila sun amince da dawo da tsarin kallon wasa a tsaye.

Kungiyar dai na neman goyon bayan Majalisa ne domin a fara gwada tsarin a wasu kungiyoyin kwallon kafa a gasar Premier.

An dai haramta tsayuwa a filin wasa saboda hadarin da ya auku a filin wasa na Hillsborugh a shekarar 1989.

A shekarar 1994 a fitar da dokar da tilastawa filayen wasa su sanya kujerun zama.

Kungiyoyon da suke goyon bayan matakin.

Aston Villa Brentford Bristol City Burnley Cardiff City Crystal Palace Derby County Doncaster Rovers Hull City Peterborough United Plymouth Argyle Watford AFC Wimbledon

A wata sanarwa da ta fitar, Hukumar kula da gasar Premier ta ce ba za ta goyi bayan tsarin ba.

Hukumar gasar Premier ta ce ba za ta baiwa gwamnati shawarar sauya tsarin hana tsayuwa a filayen wasa ba.