Soke cancanta: Sudan ta kai FIFA kara

Image caption Bajen Hukumar Kwallon kafa ta Duniya FIFA

Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Sudan ta kai karar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA gaban Kotun Saurarron kararrakin da suka shafi Wasanni ta Duniya.

Sudan dai na neman kotu tilastawa FIFA ta mayar mata da cancatarta ta shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da ta soke saboda saka dan wasan da bai cancanta ba.

Kotun ta fada ranar Laraba cewa za ta yanke hukumci kan karar a karshen watan Febrairun shekarar 2013, kafin a fara gasar.

Sudan dai za ta jagoranci rukunin D idan aka mayar mata da nasarar ci biyu da nema da ta samu kan Zambia a karawar da suka yi a birnin Khartoum a watan yuni.

Hukumar ta FIFA dai ta mikawa Zambia nasarar ci 3-0 bayan da ta yanke hukumcin cewar Saif Ali wanda ya zura wa Sudan kwallo ta biyu bai cancanci buga wasan ba saboda an bashi katinan gargadi a wasannin baya.

Karin bayani