Fifa ta tsaya a tsakiya kan batun Messi

Gofred Chitalu
Image caption Zambia ta ce Gofred Chitalu ya zira kwallaye 107 a shekara ta 1972

Hukumar Kollon Kafa ta Duniya FIFA ta ki yarda ta shiga cikin cecekucen da ake yi akan dan wasan kwallon kafa da ya yi fi jefa kwallaye a raga a shekara guda a tarihi.

Galibi an yi amannar cewa kwallo ta 86 da Lionel Messi ya jefa a wannan shekarar ta 2012, wadda ya ci ranar Lahadi ya dara bajintar da dan wasan Jamus Gerd Mueller ya yi shekaru 40 da suka shige.

Sai dai a nata bangaren, Hukumar kwallon kafa ta Zambia tana ikirarin cewa wani dan wasan kasar Gofred Chitalu ya ci kwallaye ga kungiyarsa da kuma kasarsa so 107 a shekara ta 1972.

Akan hakane kakakin Hukumar Kwallon kafa ta duniya Fifa Alex Stone, ya shaida wa BBC cewa hukumar ta Fifa ba ta adana bayanan wasannin cikin gida na kasashe.

A dan haka ikirarin da hukumar kwallon kafa ta Zambia take yi baya daga cikin bayanan tarihin da FIFA take da su.

Hukumar ta Fifa tana adana manyan wasannin kasashen da kawai take da hannu a ciki ne.

A dan Haka ba za ta iya tabbatar da bayanan da suka shafi kungiyoyin kwallon kafa na kasashe daban-daban na duniya ba.

Karin bayani