Kungiyar Marseille zata rasa Andre Ayew

andre ayew
Image caption Andre Ayew

Kungiyar kwallon kafa ta Marseille ta Faransa zata rasa daya daga cikin 'yan wasanta biyu na Ghana, 'ya'yan Abedi Pele, Andre Ayew wanda zai je gasar cin kofin kasashen Afrika.

An zabi Andre Ayew ya zama daya daga cikin 'yan wasa 26 da za a yi tankade da reraya a fitar da wadan da zasu bugawa Ghana gasar da za a yi a shekara mai zuwa, sai dai ba a sanya sunan kanin Andre din ba Jordan a cikin 'yan wasan na Ghana da aka bayyana ranar Alhamis.

Dan wasan Real Madrid Micheal Essien wanda ya bukaci a yafe masa zuwa gasar domin ya sami damar maida hankalinsa a kan kungiyarsa shi ma babu sunansa a jerin 'yan wasan.

Jerin 'yan wasan da ya kunshi 11 daga cikin 'yan wasan na Ghana da Zambia ta fitar da su daga gasar a wasan kusa da na karshe a bara za a rage su zuwa 23 bayan sun yi atisaye a Hadaddiyar Daular Larabawa inda Ghanan zata yi wasan sada zumunta da gwaji da Tunisia da kuma Masar.

Ghana zata nemi daukar kofin Afrikan ne a karo na biyar, a gasar da za a fara daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu.

Jordan da Ayew wanda yana cikin jerin wadan da aka snya sunansu domin zama zakaran kwallon kafa na Afrika na shekara, dukkannin su suna taka rawa sosai a bajintar da kungiyar ta Olympic Marseille ke yi a kakar wasanni ta bana, inda kowannen su ya ciwa kungiyar kwallaye 4 a wasanni 16. Kungiyar ita ce ta uku a gasar lig din Faransa da maki 32 a wasanni 17.