'Kadan ya rage Sunderland ta kunyata mu'

Image caption Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce 'yan wasan sa sun yi sa'a da suka tserewa shan kunya hannun Sunderland.

Kulob din na United dai ya doke Suderland ne da ci 3-1 a filin sa na Old Trafford ranar Assabar a cigaba da wasannin gasar Premier ta Ingila.

Kwallaye uku da Robin Van Persie, da Tom Cleverley da kuma Wayne Rooney suka jefa a ragar Sunderland sun baiwa kulob din damar sake darewa saman teburin gasar da tazarar maki shida.

Amma Ferguson ya ce bai ji dadin da 'yan wasansa suka kusan barin bakin nasu su farke ratar zuwa karshen wasan.

''Sunderland sun kusa cin kwallo biyu zuwa uku a karshen wasan; wanda da zai zama muzantawa sosai (a garemu)'' Inji Ferguson.

Karin bayani