An dakatar da Fellaini na Everton wasa 3

marouane, fellaini
Image caption Marouane Fellaini, ya nemi gafarar karon da ya yi wa Shawcross.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta dakatar da dan wasan Everton Marouane Fellaini daga buga wasanni uku, sabo da samun sa da laifin yiwa dan wasan Stoke City Ryan Shawcross karo.

Lamarin ya faru ne a minti na 59 a lokacin wasan Premier na ranar Asabar,wanda kungiyoyin suka tashi 1-1, a filin wasa na Britannia. A lokacin da abin ya faru alkalan wasan basu gani ba amma, na'urar da take daukan hotunan wasan ta nada.

Everton ta yanke shawarar cewa ba zata daukaka kara ba a kan hukuncin abin da ke nufin cewa ta yarda dan wasan ba zai buga wasanta da West Ham da Wigan da kuma Chelsea ba.

Kocin Everton David Moyes da kansa ya soki lamirin dan wasan nasa kan abin da ya yi bayan an kammala wasan inda ya ce abu ne da bai dace ba ko alama kuma ya yi tsammanin daman za a hukunta shi.

Shi ma Fellaini, dan shekara 25 ya ce ya baiwa Ryan Shawcross hakuri a kan lamarin da sauran 'yan wasan kungiyar tasa da masu goyon bayansu, ya ce ya harzuka ne a lokacin kuma hakan bai dace ba.