Katongo ne zakaran kwallon Afrika na BBC

christopher, katongo
Image caption Christopher Katongo, ya taimakawa Zambia kan nasarar da ta samu ta daukar kofin Afrika.

Kyaftin din Zambia Christopher Katongo, ya sami nasarar zama zakaran kwallon kafa na Afrika na BBC na shekarar 2012.

Dan wasan mai shekara 30 ya sami galaba ne akan Demba Ba da Didier drogba da Younes Belhanda da kuma Yaya Toure, inda ya zama dan wasa na farko daga kudancin Afrika da ya taba samun wannan nasara.

Kwararru a fagen kwallon kafa ne dai daga kowace kasa a Afrika suka zabo sunayen 'yan wasan bisa gwaninta da kwarewa da kuma natsuwar kowannensu a wasan.

Kuma mutane da dama ne suka zabi wanda suke ganin ya fi can-cantar samun matsayin ta hanayar kada kuriarsu ta intanet da kuma ta sakon wayar salula, inda sama da kashi 40 cikin dari na wadan da suka yi zaben su ka zabi Katongo, wanda ya ke bugawa kungiyar Henan Construction ta China.

Dukkanin 'yan wasan da aka zaba a wannan gasa sun taka rawar a zo a gani a wasanninsu inda hudu daga cikinsu suka sami lambobin azurfa,to amma Katongo ne masu sha'awar wasan kwallon kafa a Afrika ke ganin nasarar da ya samu da irin rawar da ya taka ta wuce ta sauran.

Katongo wanda kuma soja ne a kasarsa ya taimakawa kasar tasa sosai wajen samun nasarar daukan kofin Kasashen Afrika na farko a watan Fabrairu.

Ya ciwa Zambian kwallaye 3 kafin su kai ga wasan karshe a gasar kasashen Afrikan a Equitorial Guinea da Gabon sannan kuma a wasan karshe da Ivory Coast ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya baiwa Zambian nasara da ci 8 -7 ta dauki Kofin a Libreville.

Karin kokarinsa

Watanni bakwai bayan ya jagoranci kasarsa zuwa ga nasarar daukar kofin kasashen Afrikan, Katongo ya sake taimakawa Zambian a wasan neman shiga gasar cin Kofin na Afrika a karawar karshe zagayen farko da kasar Uganda inda ya jefa kwallo daya tilo a raga ta wannan karawa, kuma wannan kwallo ita ta taimakawa Zambia inda a zagaye na biyu, Uganda ta ci Zambia daya ba ko daya da hakan yasa aka kai ga bugun daga kai sai maitsaron gida tsakanin kasashen biyu kuma Zambian ta sami nasara da ci 9-8.

A tsakanin wannan bajinta da ya nuna a wasannin cin Kofin Afrika, Christopher Katongon ya kuma taka rawar a zo a gani wajen fitar da Zambia daga halin kaka-ni-kayi a wasanninta na neman zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2014.

Zambia ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Sudan a Khartoun a watan Yuni, sakamakon da har yanzu ake tababa a kansa kasancewar ana zargin Sudan da sanya dan wasan da bai cancanta ba, mako daya daga nan Zambian ta na matukar bukatar samun nasara a kan Ghana domin cigaba da kasancewa a kan turbar zuwa gasar Kofin Duniya, inda nan ma Katongon ne ya ciwa Zambian kwallon da ta bata nasara.

Ana ganin dai in har Christopher Katongon zai cigaba da wannan kwazo da ya kai kasarsa zuwa matakin da bata taba kaiwa ba da kuma sunan da shi ma ya yi , to kuwa ba shakka zai iya kai Zambian matakin da ya fi kowana mataki a Brazil a watanni 18 masu zuwa,a gasar cin Kofin Duniya.