An dakatar da shugaban FA na Afrika ta Kudu

kirsten, nematandana
Image caption Kirsten nematandana, na fuskanatar zargin coge a wasanni domin amfanin 'yan caca.

An dakatar da shugaban Hukumar kwallon Kafa ta Afrika ta Kudu Kirsten Nematandani da wasu manyan jami'ai hudu sakamakon wani rahoton Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, a kan badakalar chogen wasanni.

An raba jami'an ne da mukamansu yayin da ake gudanar da bincike a kan rawar da ake zargin sun taka a chogen wasannin sada zumunta da Afrika ta Kudu ta yi na shirye shiryen tunkarar gasar cin Kofin Duniya da aka yi ta 2010.

Binciken FIFA a kan ayyukan mutumin nan da ya yi suna wajen badakalar chogen wasanni dan kasar Singapore, Wilson Perumal, da kungiyarsa ta Football 4u ya nuna yadda jami'an Hukumar Kwallon Kafar ta Afrika ta Kudun su biyar ke da hannu a cuwa-cuwar wasannin kamar yadda aka bada bayani a wani taron manema labarai.

Sakamon wasannin da Afrika ta Kudu ta yi da kasashen Thailand da Bulgaria da Colombia da kuma Guatemala da suka yi makwanni kafin a fara gasar ta Kofin Duniya ta 2010 an gano cewa an tsara su ne domin amfanin wata kungiyar 'yan caca dake Asia.