Arsenal ta lallasa Reading da ci 5 da 2

'Yan wasan kulob din Arsenal
Image caption 'Yan kulob din Arsenal na murnar samun nasara a kan Reading

Kulob din Arsenal ya fara murmurewa daga jinjikin da kulob din ya yi a hannun Bradford City a gasar League one na Carling cup.

Hakan ya biyo bayan nasarar da Arsenel ta samu a kan kulob din Reading.

Lukas Podolski ne ya fara jefa kwallo a ragar Reading, kuma Gunners sun samu zura kwallaye hudu a cikin sa'a guda, bayan Santi Cazorla ya zamo dan spaniya na uku da ya zura kwallaye uku a wasa daya na gasar Premier League.

Fernando Torres da Jordi Gomez ne sauran spaniyawan biyu da suka kafa wannan tarihin.

Biyo bayan lallasa Reading da Arsenal ta yi a wasan, hakan ya sa ba a tsammanin kulob din zai dawo gasar, a yayin da Adam Le Fondre da Jimmy Kebe suka zura kwallaye biyu a cikin mintoci biyar.

Reading na fuskatar barazanar ficewa daga Premier League, inda kulob din ke cigaba da kasancewa a kasan teburin da maki shida.