Kocin Kenya ya ajiye aiki bayan watanni 3

henry, michel
Image caption Henry Michel, ya ajiye aikin kocin Kenya a watanni uku.

Tsohon kocin kwallon kafa na Faransa Henri Michel ya ajiye aiki a matsayin mai horadda 'yan wasan Kenya, watanni uku bayan nada shi a mukamin.

Kocin ya ajiye aikin ne bisa dalilan da ya bayar na bambamce-bambamce game da yarjejeniyar kwantiraginsa.

Karkashin jagorancin kocin dan shekara 65, kenya ta yi rashin nasara a wasanninta biyu na sada zumunta a dan takaitaccen lokacin da ya rike mukamin, kafin ya ki zuwa da 'yan wasan kasar babbar gasar cin kofin kalubale na yankin gabashi da tsakiyar Afrika da aka yi a Uganda a wannan watan inda Kenyan ta zama ta biyu.

Wannan dai shi ne ya kawo karshen wani aikin na horadda 'yan wasan wata kasa da Michel din wanda ya rike irin wannan matsayi na koci a kasashe 12 tun bayan da ya bar aikinsa na horad da 'yan wasan Faransa a 1988.

Kocin dan kasar Faransa ya je gasar cin Kofin Duniya har sau hudu da kungiyoyin kasashe hudu, farko da Faransa a 1986 sai Kamaru a 1994, sannan Morocco a 1998 sai kuma a 2006 inda ya je da kasar Ivory Coast.

Haka kuma ya zama kocin 'yan wasan Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Tunisia.

Yanzu dai kenyan ta maye gurbinsa da James Nandwa.