Yaushe Messi zai bar Barcelona?

lionel_messi
Bayanan hoto,

Lionel Messi, zai ci gaba da kasancewa a Barcelona har 2018.

Lionel Messi ya amince ya sabunta kwantiraginsa da Barcelona har zuwa shekara ta 2018.

Dan wasan dan kasar Argentina, mai shekara 25 ya sami yin bajinta ga kungiyar ta Barcelona da kuma kasarsa a wannan shekara, inda ya jefa kwallaye 90 a raga.

Messi ya ciwa Barcelona kwallaye bibbiyu a kowana wasa da ya buga wa kungiyar takwas na karshen shekaran nan.

Shi ma dan wasan baya na kungiyar Carles Puyol, mai shekaru 34 da dan wasan tsakiya Xavi Hernandez mai shekaru 32 dukkanin su sun amince su cigaba da zama a kungiyar ta Barcelona har zuwa 2016.

A cikin makwannin da ke tafe ne 'yan wasan za su sanya hannu a sabbin kwantiragin nasu kamar yadda kungiyar ta tabbatar.

Wannan dai na nufin cewa Barcelonan ta sami nasarar cigaba da kasancewa da muhimman 'yan wasanta uku.

Messi wanda ya ke Barcelona tun yana dan shekara 13, ya fara bugawa klub din wasan lig na farko a wasansu da kungiyar RCD Espanyol ranar 16 ga watan Oktoba na 2004.

A wannan shekara ta 2012 Messi ya kasance kan ganiyarsa ta cin kwallo inda ya zarta bajintar dan wasan Jamus Gerd Mueller ta shekara 40 ta jefa kwallaye 85 a raga a cikin watanni 12,a lokacin wasan Barcelona da Real Betis ranar 9 ga watan Disamba da kungiyar tasa ta ci 2-1.

Messi ya kara yawan kwallayen da ya ci a shekarar zuwa 90 ranar Lahadi, da wasu kwallayen biyu da ya jefa a ragar Atletico Madrid a karawarsu wadda Barcelona ta yi nasara 4-1.

Yana daga cikin 'yan wasan da ke saran zama Gwarzon dan kwallon kafa na Duniya a karo na hudu, inda aka sanya shi a jerin 'yan wasa uku Cristiano Ronaldo da Andres Iniesta na Barcelona wadan da ake saran zabar daya daga cikinsu domin samun wannan matsayi.