Kungiyar Napoli zata daukaka kara

paolo, cannavaro
Image caption Paolo Cannavaro, an dakatar da shi watanni shida.

Kungiyar Napoli zata bi kadin hukuncin da Hukumar Kwallon Kafa ta Italiya ta yi na yanke mata maki biyu da kuma dakatar da 'yan wasanta Paolo Cannavaro da Gianluca Grava na tsawon watanni shida.

An yankewa Kungiyar ne ta Italiya ta rukunin Serie A, maki biyu tare da dakatar da 'yan wasan nata biyu sabo da laifin cuwa-cuwar coge a wasa.

Shi ma tsohon mai tsaron gidan kungiyar ta Napoli, Matteo Gianello mai shekara 36, an dakatar da shi daga wasa har tsawon watanni 39 sabo da ya amince cewa ya so ya yi coge a wasan Napolin da Sampdoria a 2010.

An ki amincewa da bayanan Cannavaro mai shekara 31, da Grava dan shekara 35, aka kuma yanke musu wannan hukunci sabo da sun ki bada rahoton makarkashiyar tsohon mai tsaron gidan Gianello ta yin cogen a lokacin.

Haka kuma Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Italiya ta ci tarar klub din fam 57,000.

Sakamakon maki biyun da aka yankewa kungiyar ta Napoli wadda ke saran kaiwa ga nasarar daukan kofin gasar Serie A, yanzu ya zama maki 10 ne tsakaninta da Juventus wadda ke kan gaba a gasar, kuma ta dawo baya daga matsayi na uku zuwa na biyar.

A da dai Cannavaro wanda tsohon dan wasan Parma ne wanda ya ke kungiyar ta Napoli tun 2006 da Gravan wanda ya dawo kungiyar a 2005, dukkanninsu sun ki yarda da cewa suna da hannun a badakalar.

Yanzu dukkansu ba zasu buga sauran wasannin da suka rage na gasar ta Serie A ba sai dai in sun daukaka kara kuma suka sami nasara.

Gagarumin binciken da aka gudanar na laifuka da yin coge a wasanni saboda masu cacar wasanni a kasar ta Italiya ya sa an kama mutane da kuma dakatar da 'yan wasa da kungiyoyi da yawa.

A wani lamarin na daban kuma an dakatar da kocin Juventus Antonio Conte tsawon watanni goma sabo da kin bada rahoton cogen wasa lokacin yana koyarda kungiyar Siena wadda a lokacin ta ke rukunin Serie B a kakar wasanni ta 2010-11.