Magoya bayan Zenit 'yan wariya ne -Samba

christopher samba
Image caption Christopher Samba,'' magoya bayan zenit ba su da da'a''.

Dan wasan baya na kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha, Christopher Samba dan kasar Congo-Brazzaville, ya ce magoya bayan kungiyar Zenit ta St Petersburg ta Rasha, ba su san yakamata ba kuma 'yan wariyar launin fata ne da ke rayuwa a wani karni na daban.

Dan wasan ya furta wadan nan kalamai ne sakamakon kiran da babbar kungiyar magoya bayan kungiyar ta Zenit St Petersburg suka yi na kada klub din nasu ya dauki wani dan wasa bakar fata ko masu neman maza, inda suka ce tilastawa kungiyar aka yi ta dauki bakar fata.

Samba ya ce ko alama shi bai yi mamaki ba domin kowa ya san magoya bayan kungiyar ta St Petersburg cewa ba su da kamala kuma 'yan wariyar launin fata ne.

Christopher Samba ya kara da cewa ''a wannan zamani mu na da al'ummomi da kasashe daban daban da su ke da kungiyoyi .Idan ba zasu amince da haka ba to kuwa ba zasu cigaba ba''.

Zenit ita ce babbar kungiya daya ta kasar Rasha da ba tada dan wasa bakar fata in ban da a kakar wasannin nan da ta dauki dan kasar Brazil Hulk, da kuma dan kasar Belgium Axel Witsel.

A shekarar 2011 Hukumar kwallon kafa ta Rasha ta ci tarar kungiyar ta Zenit bayan da wani magoyin bayanta ya baiwa dan wasan Anzhi Makhachkala, Roberto Carlos, ayaba kafin karawar kungiyoyin.

'yan wasa bakaken fata a lig din Rasha su na fama da matsalar wariyar launin fata inda akan kwatan ta su da biri.

Wani magoyin bayan kungiyar Lokomotiv Moscow ya taba jefawa Samba ayaba lokacin bai dade da dawowa kungiyar ba daga Blackburn Rovers.

Karin bayani