An dage wasannin kwallon kafa a Scotland

Wasan kwallon kafa
Image caption Wasan kwallon kafa

An dage wasu gasar wasannin kwallon kafa a kasar Scotland, sakamakon ruwan da ya mamaye filin wasan.

Ana dai shan dage gasar wasannin kwallon ne, sakamakon yanayin marka-markar ruwan saman da ke shafar harkokin gudanar da wasan.

Gasar wasannin kwallon kafa kimanin shida ne da wasu wasanni bakwai suka fuskanci irin wannan tsaiko a baya, sakamakon irin wannan matsala.

Ko a ranar Juma'a ma sai da aka dakatar da gasar wasan kwallon Scotland rukuni na daya, tsakanin kungiyar Dumbarton da Raith Rovers.

Wadanne wasanni ne aka dage?

Wasan Zakaru: Tsakanin Blackburn da Brighton

Rukunin Lig na daya: Tsakanin Brentford da Stevenage, Crewe da Bournemouth, Doncaster da MK Dons, Hartlepool da Portsmouth, Notts County daLeyton Orient, sai kuma tsakanin Scunthorpe da Carlisle

Rukunin Lig na biyu: Tsakanin Bristol Rovers da Rotherham, Morecambe, Dagenham da Redbridge, Oxford Utd da Fleetwood Town, Port Vale da Wimbledon, Torquay da Exeter, Wycombe da Bradford, sai kuma York da Gillingham.

Gasar wasan kwallon Scotland Rukuni na daya : Tsakanin Dumbarton da Raith Rovers

Gasar wasan kwallon Scotland Rukuni na: Tsakanin Ayr da Brechin