Osaze ya mayar da martani ga Steven Keshi

Osaze
Image caption Peter Osaze yana haskaka wa sosai a West Brom

Dan wasan Najeriya Peter Osaze Odemwingie ya mayar da martani cikin fushi bayan da kocin Najeriya Steven Keshi ya ki sanya sunansa a cikin tawagar kasar ta gasar cin kofin kasashen Afrika.

Odemwingie wanda ke taka leda a West Bromwich Albion, ya buga wasansa na baya-bayan nan ne a Najeriya, a wasan da kasar ta tashi 0-0 Rwanda a wasan share fagen shiga gasar cin kofin Afrika a watan Fabreru.

Kowanne koci na da nasa tsarin da kuma shiri - idan ban dace da tsarinka ba, sai ka fito fili ka gayamin," kamar yadda Odemwingie ya shaida wa BBC.

Dan wasan mai shekaru 31 ya halarci gasar cin kofin kasashen Afrika a 2004, 2006, 2008 da 2010.

Jerin 'yan wasa

"Na shafe shekaru goma ina bautawa Najeriya a matsayin dan wasa, ina taka leda saboda da kasar da kuma magoya baya, bawai don wani mutum ba.

"Saboda ina fitowa fili na fadi gaskiya idan ba'a yi daidai ba, shi yasa wasu mutane ba sa jin dadin abinda nake yi."

Najeriya za ta buga wasanta na farko ne da Burkina Faso ranar 21 ga watan Janairu sannan ta fafata da Zambia da kuma Ethiopia a rukunin C.

Jerin 'yan wasa 32 da Najeriya ta gayyata domin tantancewa:

Masu tsaron gida : Vincent Enyeama (Maccabi Tel Aviv, Israel); Austin Ejide (Hapoel Be'er Sheba, Israel); Chigozie Agbim (Enugu Rangers); Daniel Akpeyi (heartland)

'Yan baya : Elderson Echiejile (FC Braga, Portugal); Juwon Oshaniwa (Ashdod FC, Israel); Benjamin Francis (Heartland); Joseph Yobo (Fenerbahce, Turkey); Efe Ambrose (Celtic, Scotland); Solomon Kwambe (Sunshine Stars); Azubuike Egwuekwe (Warri Wolves); Danny Shittu (Milwall, England); Kenneth Omeruo (ADO Den Haag, Netherlands); Godfrey Oboabona (Sunshine Stars)

'Yan tsakiya : John Mikel Obi (Chelsea, England); Nosa Igiebor (Real Betis, Spain); Ogenyi Onazi (Lazio, Italy); Raheem Lawal (Adana Demirspor, Turkey); Obiora Nwankwo (Calcio Padova, Italy); Fegor Ogude (Valerenga FC, Norway); Reuben Gabriel (Kano Pillars); Rabiu Ibrahim (Celtic FC, Scotland)

'Yan gaba : Ahmed Musa (CSKA Moscow, Russia); Emmanuel Emenike (Spartak Moscow, Russia); Brown Ideye (Dynamo Kyiv, Ukraine); Victor Moses (Chelsea, England); Uche Kalu (Rizespor, Turkey); Bright Dike (Portland Timbers, USA); Shola Ameobi (Newcastle United, England); Ikechukwu Uche (Villarreal FC, Spain); Ejike Uzoenyi (Enugu Rangers); Sunday Mba (Enugu Rangers)

Karin bayani