Keshi zai fuskanci matsala a kan Ameobi

Shola Ameobi
Image caption A karkashin dokar FIFA, kulob-kulob na kasashen waje ba za su rike wani dan wasa ba, a lokacin gasar cin kofin zakarun Afrika

Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Stephen Keshi ya ce zai fuskanci matsala kan barin Shola Ameobi ya yi wasa a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika.

Manajan kulob din Magpies, Alan Pardew ya hakikance cewa dan wasan gaban ba zai je kasar Afrika ta Kudu ba.

Keshi yace " Da alamu a cikin kwantiraginsa, akwai inda aka ce ba zai bar kulob din ba don buga wasa a gasar cin kofin nahiyar Afrika."

Har ila yau game da kiran 'yan wasan da za su takawa Najeriya leda, hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce za ta mika kokenta gaban FIFA, idan ba a bar dan wasan baya, Danny Shittu ya shiga gasar ba.

Duka 'yan wasan biyu dai na cikin jerin 'yan wasa 32 da ake so su buga wasan karshe a gasar wanda za a yi daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairun shekarar 2013.

Sai dai Keshi bai fitar da ran cewa Ameobi zai buga wa kasarsa wasa ba.

Ya ce "Na yi magana da Ameobi kuma ya shaida mini cewa manajansa baiyi magana da shi ba, kafin ya yi jawabi ga manema labarai."

"Kuma yace zai yi magana da manajan nasa bayan karawarsu da Manchester United, sannan zai tuntube ni."