Drogba zai jagoranci 'yan wasan Ivory Coast

Didier Drogba
Image caption Didier Drogba

Dan wasan nan Didier Drogba ne zai jagoranci kungiyar kwallon kafar Ivory Coast zuwa gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika a watan Janairun 2013.

Haka kuma kungiyar ta kira dan wasan gaba na kulob din Wigan Athletic, wato Arouna Kone don takawa kasarsa leda.

Kone ya yi wasa a zagayen karshe na gasar zakarun Afrika da aka yi a shekarun 2006 da 2008.

Sannan kungiyar ta kunshi dan wasan tsakiya dake zaune a Spaniya, Romaric, wanda shi ma ya dan kwana biyu bai buga wasa a gasar ba.

Kone na daya daga cikin 'yan wasa shiga dake taka leda a gasar Premier League da aka sanya a kungiyar ta Ivory Coast.

An kira 'yan wasa uku gida da suka hada da 'yan wasan da suka fito daga iyalan Toure da kuma Abdul Razak, yayin da Arsenal kuma ta yi rashin Gervinho, sai Cheick Tiote daga Newcastle, wadanda duka za su buga wa kasarsu ta haihuwa wasa.

Kasar Ivory Coast ita ce ta biyu, wajen bayyana kammala hada 'yan wasanta da suka kunshi mutane 23, domin fafatawa a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika da za a yi a Afrika ta kudu.